
Rahotanni sun bayyana cewa, Dangote ya janye zargin da yakewa shugaban Hukumar NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmad a gaban Hukumar ICPC.
Dangoten ya janye zargin da yake wa Ahmad ne inda yace ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa ‘ya’yansa kudin makaranta a kasar Switzerland.
Wata Majiya tace Dangoten ya janye zarginne bayan da aka bukaci ya je da kansa ba aiken Lauya ba ya gabatar da hujjoji a gaban ICPC kan wannan zargin da yake.
Hakanan Wata Hujja da aka samu game da janye wannan korafi da Dangoten yayi shine EFCC ta fara bincike kan lamarin.
Saidai ICPC tace duk da wannan Janyewar da Dangote yayi ba zata yi watsi da binciken da takewa Ahmad ba, tace ta ma aika da bukatar bincike makarantar da ake zargin Ahmad din ya kai ‘ya’yansa.
Ahmad dai tun tuni ya sauka daga kan mukaminsa bayan wannan zargin da Dangote ya masa.