
Wani Bidiyo ya bayyana da ya nuna dan Damben Najeriya, Anthony Joshua yana waya tare da dayan dan damben Najeriyar, Kamaru Usman bayan Khadarin motar da ya rutsa dashi da abokansa.
A Bidiyon an ga yanda Kamaru Usman kewa Anthony Joshua jaje inda yake ce masa ya girgiza mutanen Duniya.
An ga Anthony Joshua yana dariya a Bidiyon.
Saidai Bidiyon ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa me zai sa Anthony Joshua ya rika dariya ko dai tsafi yayi da abokan nasa biyu da suka rasu a hadarin?
Wasu kuma sun bayyana cewa bai kamata ace an dauki Bidiyon wayar da suka yi din ba.
Saidai bayan da cece-kucen da Bidiyon ya jawo, Kamaru Usman ya fito ya bayar da hakuri.
Yace shine ke da laifi domin akan daukar Bidiyon domin a lokacin yana shirin yin wani dambene ya daga waya yana kiran Anthony Joshua kuma dama ana daukarsa Bidiyon.
Yace shine ya kamata ace ya duba an cire daidai inda suka yi magana da Anthony Joshua kamin a wallafa Bidiyon.