
Rahotanni sun bayyana cewa, Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka aikawa matar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Watau Remi Tinubu da tallafin data nema na zagayowar ranar Haihuwarta.
Remi Tinubu ta nemi a tara mata kudi a yayin data cika shekaru 65 da haihuwa inda tace za’a yi amfani da kudin wajan kammala ginin hedikwatar dakin karatu na kasa.
Tuni aka sanar cewa kudin sun kai sama da Naira Biliyan 20 wadanda ‘yan Najeriya suka tara mata.
Saidai wani abin mamaki shine, cikin jerin mutanen da suka tura mata da kudaden tallafin hadda tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.
Hakan na zuwane duk da cewa, tun kamin Uwargidan shugaban kasar ta fara neman wannan tallafin Buhari ya rasu.
Abin ya zowa mutane da yawa da mamaki matuka.
Sauran wadanda suka turawa matar shugaban kasar tallafin sune, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Mataimakinsa, Kashim Shettima, Kakakin Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio, dana Wakilai, Tajudeen Abbas da sauransu.