
A yayin da rikici tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti ke ci gaba da gudana inda take zarginshi da neman yin lalata da ita, shidai bai ce komai ba kan lamarin har yanzu.
Saidai ‘yan Koronsa sun dukufa aiki inda a yanzu haka sun bankado bayanai akan rayuwar sanata Natasha a baya.
Daya daga cikin abubuwan da suka gano shine cewa, Mijinta da take aure sai da ya mata cikin shege ya zubar dashi sannan suka yi auren.


Hakan ya bayyanane a cikin takardar karar data kai Mijin nata me suna Uduaghan wanda takardar kotun data watsu sosai a kafafen sada zumunta ta nuna cewa ya mata alkawarin aure kamin ta yadda yayi lalata da ita har ta dauki ciki.
Saidai bayan data dauki cikin, ta ga Alamar ba shi da niyyar aurenta inda anan ya nemi ta zubar da cikin amma ta kiya, dalili kenan da ya hada baki da kukunsa suka zuba mata maganin zubar da ciki a abinci taci bata sani ba cikin ya zube.
Dalilin haka, Sanata Natasha ta makashi a kotu, inda kuma ta gano cewa bai saki tsohuwar matarsa ba saboda ya aureta kamar yanda ya mata alkawari.
Hakanan a takardar kotun, Sanata Natasha Akpoti ta bayyana cewa, Mijin nata wanda a lokacin da ta yi wannan karar basu yi aure ba, ya sa ta bar duk wani kasuwanci da take yi ta mayar da hankali kan soyayyarsa da sunan cewa zai aureta amma gashi yana shirin yaudararta.
Saidai ba’a san yanda lamarin ya kare ba gashi dai sun yi aure suna zaune a matsayin mata da miji.
Ana zargin magoya bayan Sanata Godswill Akpabio ne suka bankado wannan takardar kotun da Sanata Natasha Akpoti ta taba yin karar mijin nata tun kamin su yi aure.
Zuwa yanzu dai sanata Natasha bata ce komai ba kan lamarin.