
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shiga fadar shugaban kasar dake Abuja.
Saidai a martanin da fadar shugaban kasar ta fitar ta bakin me magana da yawun shugaban kasar, Stanley Nkwocha yace wannan magana karyace da wasu suka kirkira dan cimma wata manufa.
Ya kara da cewa babu wani abu me kama da wannan da ya faru a fadar shugaban kasar.
Yace hankalin mataimakin shugaban kasar na kan aikin da yake gabansa na gina kasa.
Hakanan ya kawo bayanai akan wata karya da aka yada a baya ta fastar yakin neman zaben shugaban kasar da mataimakinsa wanda yace basu da alaka dashi.