
A wani lamari mai kama da na ba-zata a fagen siyasar Najeriya, sunan tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya sake dawowa yake amo, musamman bayan alamu sun fara nuna akwai ɓaraka a tsakanin makusantansa.
Alamu sun fara bayyana ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar SDP, inda ya ce da amincewar tsohon shugaban ƙasar ya sauya sheƙar ta siyasa.
Sai dai daga baya Buhari ya fito ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, cewa shi ɗan APC ne, kuma yana alfahari da kasancewarsa ɗan jam’iyyar, inda ya ce yana godiya ga magoya bayan APC, sannan zai yi duk mai yiwuwa domin samun nasararta.
Sai dai daga lokacin aka samu wata goguwar siyasa ta tashi a ƙasar, inda aka fara maganar jiga-jigan ƴansiyasar ƙasar za su koma SDP domin a samu haɗakar da za ta ƙalubalanci APC.
Haka kuma ziyarar da Atiku Abubakar ya jagoranci su Nasir El-Rufai da wasu makusantan Buhari ya sake rura maganar, duk da cewa Atiku ya ce ba siyasa ta kai su ba, ziyara ce ta gaisuwar sallah.
Amma shi ma shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci shugabannin jam’iyyar zuwa gidan na Buhari a Kaduna, sannan ya bayyana bayan ziyarar cewa su yayyafa wa ziyarar su Atiku ruwan sanyi.
‘Abin da ya sa muka jaddada goyon baya ga Tinubu’
A daidai lokacin da ake raɗe-raɗin wasu jiga-jigan ƴansiyasar ƙasar za su haɗe domin ƙalubalantar APC ɗin kuma wasu ƴan tsohuwar jam’iyyar CPC, waɗanda ake ganin makusanta Buhari ne suka fito suka barranta kansu daga sabuwar tafiyar siyasar.
Ƴan siyasar waɗanda suka fito a ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-Makura, sun jaddada goyon bayansu ne ga jam’iyyar APC da kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin waɗanda suka harci taron har da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da tsohon ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da Farouk Adamu Aliyu, tsohon ɗan majalisar daga jihar Jigawa da wasu ƙusushin tsohuwar CPCn.
A sanarwar da suka fitar, sun yi watsi tare da musanta zargin rashin jin daɗin APC da kuma rahotannin da ke cewa za su fice daga jam’iyyar.
Sai dai a ciki sun yi kira ga shugabancin APC da ya yi tafiya da dukkanin ɓangarorin jam’iyyar a kowane mataki.
Farouk Adamu Aliyu yana ɗaya daga cikin ƴan tsohuwar CPC ya bayyana a hirarsa da BBC cewa inda ya ce wani ɓangare ne na CPC ne da suke tunanin abubuwa ba sa tafiya yadda suke so, suka ari bakinsu suka ci musu albasa cewa ba sa tare da Tinubu.
Ya ce “Shi ya sa muka ga ya dace mu sanar wa jama’a, mu ilahirin waɗanda muka taho a cikin jam’iyyar CPC wadda ta haɗe ta zama APC cewa muna nan daram tare da gwmanatin Tinubu kuma za mu yi duk abin da za mu iya domi jam’iyyarmu ta kai ga nasara.”
Ba da yawunmu aka yi ba – Malami
Sai dai a lokacin da ake tattauna batun jaddada goyon bayan ƴan CPCn ga gwamnatin Tinubu, sai tsohon Ministan Shari’a na Najeriya, wanda daya ne daga cikin jami’an tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari mafi karfin fada a ji, wato Abubakar Malami, SAN, ya yi watsi da iƙirarin.
A cikin wata sanarwa da kakakin tsohon ministan, Muhammad Bello Doka ya fitar, ya ce jagorancin tsohuwar jam’iyyar CPCn ne kawai ke da alhakin fitar da matsayar tsohuwar jam’iyyar kan batun fita daga APC, ba tsagin su Almakura ba.
Malami ya zargi Tanko Al-Makura da Adamu Adamu da Aminu Bello Masari da kuma Farouk Adamu Aliyu da janye jikinsu daga jikin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
Dangane da batun komawar sa jam’iyyar SDP kuwa, Malami ya ce aikin masu yaɗa jita-jita ne, amma ya ce yana kan tattaunawa da magoya bayansa game da batun.
“Malami fitaccen mutum ne a Najeriya, don haka ba zai fice daga jam’iyya a asirce ba, har yanzu yana APC, amma yana ci gaba da tattaunawa da magoya bayansa, idan ya kammala kuma zai bayyana matsayarsa”, in ji kakakin tsohon ministan.
Abin da ya jawo ɓarakar – Masani
A game da yadda lamarin yake tafiya, BBC ta tuntuɓi mai sharhi kan harkokin yau da kullum da siyasa a Najeriya, Bashir Hassan Jantile, kan yadda aka fara ganin ɓaraka a tsakanin makusantan na Buhari, wanda ya ce al’amari ne mai sauƙin fahimta.
A cewarsa, “a ganina babu wata dambarwa, domin kowa yana bayani ne a matsayin da yake kai. Misali Faruk Adamu Aliyu ai babu jayayya idan aka yi maganar Buhari a shekara 20 da suka gabata su ne a gaba a cikin abokan tafiyarsa.”
Sai dai ya ce yanzu abubuwa sun canja, inda a cewar Jantile daga lokacin da Buhari ya hau mulki, ya yi shekara takwas zuwa yanzu akwai wasu jiga-jigan da suka fi kusanci da shi.
“Idan ana maganar Buhari a yanzu, matuƙar ba ka ga Isa Ali Pantami ba ko Hadi Sirika ba ko Abubakar Malami ba, to wannan wasa ne kawai,” in ji shi.
A game da zargin cewa tsagin da suka nuna goyon bayansu ga gwamnatin Tinubun suna da wata alaƙa da gwamnatin ne, Jantile ya ce hakan ne ma ya sa bai ga laifinsu ba don sun kare gwamnatin.
“Abin da suka yi, sun yi daidai, amma ba su da ƙarfin su Malami a wajen Buhari a yanzu.”
A game da inda matsalar ta fito, Jantile ya ce Bola Tinubu ne tushen dambarwar tun a farko.
“Shugaba Bola Tinubu ba ya ya yin wasu abubuwa na zahiri tare da Buhari. Misali a zamanin Buhari akwai sanannun yaran Tinubu irin su Osinbajo da Fashola a gwamnati, amma a yanzu babu yaran Buhari a gwamnatin Tinubu.”