
Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa akalla dalibai 6 ne suka rasu bayan bullar wata cuta da ba’a san kalarta ba a jami’ar kimiyya da fasa ta jihar me suna Kebbi State University of Science and Technology, Aleru.
Rahoton yace wasu kuma na can kwance ba lafiya a asibiti.
Rahoton yace duk da ana samun karuwar yawan daliban dake dauke da wannan cuta amma hukumomin makarantar sun ki su kulleta wanda hakan ya jefa iyayen dalibai cikin damuwa
Wasu daliban makarantar sun koka da faruwar lamarin inda suka ce yana da alaka da rashin daukar mataki na hukumomin makarantar.
Rahoton yace ba a makarantar kadai lamarin ya faru ba hadda ma cikin gari inda cutar ta kashe mutane da dama.
An bayyana cutar da cewa yawanci ana korafin ciwon wuyane wanda kuma nan da nan sai mutum ya fita hayyacinsa sai ya mutu.
Tuni dai jami’ar ta baiwa dalibai shawarar su dauki matakan kare kansu daga wannan lamari inda kakakin jami’ar, Mustapha Mansur Ango yace dalibai su rika kwanciya a guri me wadataccen iska sannan su rika tsaftace muhallinsu da kula da wanke hannu.