
Rahotanni daga kasar Congo sun bayyana cewa, wata sabuwar cuta da ba’a santa ba ta kashe mutane akalla 50.
Hukumar lafiya ta Duniya, WHO ce ta bayyana hakan inda tace cutar na kuma ci gaba da yaduwa.
Mahukunta a kasar na hada kai da hukumar ta WHO dan yin bincike akan wannan sabuwar cuta.
Zuwa yanzu, cutar ta kama mutane 431 wanda kuma daga ciki mutane 53 sun mutu.
Rahoton yace an fara ganin cutar ne a jikin wasu yara ‘yan kasa da shekaru 5 su 3 wadanda suka fara nuna alamun cutar bayan cin mataccen Jemage.
Alamomin cutar sun hada da Ciwon kai, Zazzabi, Zawo, da kasala. Kuma yawanci cutar na kisa ne kwana biyu bayan an kamu da ita.
Yanayin garuruwan da mutanen ke kamuwa da cutar wanda babu wadatattun asibitoci ne yasa ake samun saurin yaduwar cutar inji WHO.