
Mutane 6 ne suka mutu a wani rikici da ya kunno kai tsakanin Al’ummar Ezza dake karamar Hukumar Ado a jihar Benue da kuma makwabtansu Effium na dake jihar Ebonyi.
Wannan rikici ya dauki shekara da shekaru yana faruwa inda aka yi iya kokari dan kawo karshen shi amma lamarin ya faskara.
Wata majiya daga yankin tace rikicin kwanannan ya barkene ranar Asabar da misalin karfe 2:30 p.m. inda wasu ‘yan Bindiga da aka yi amannar daga Effium suke suka afkawa garin Ezza.
‘Yan Bindigar sun bude wuta inda suke harbin kan mai uwa da wabi.
Rahoton yace maharan sun kuma afkawa kayan mutane da sata.
Kokarin jin ta bakin kakakin ‘yansandan jihar ya ci Tura.