
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi hasashen cewa watarana za’a samu musulmi ya zama shugaban kasar Amurka.
Ya bayyana hakane bayan da Musulmi na farko, Zohran Mamdani ya zama magajin garin New York City na kasar.
Malam ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook inda yake cike da farin ciki.