Wednesday, January 15
Shadow

Wuridin kudi nan take

Musulunci ya amincewa mutum ya roki Allah Arzikin Duniya da ya hada da Kudi, Mata ta gari, da sauransu.

Tirmizi ya ruwaito daga Sabit, Anas yace, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi waslalam yace “Kowannenku na da damar ya roki Allah dukkan abinda yake so, hadda rokon Allah madaurin takalmi idan ya katse.

Albani ya inganta wannan hadisi.

Wannan na nuni da cewa komai mutum zai roka ya roki Allah, saidai a nemi Albarka a cikin rayuwar Duniya da dukiyar da kuma Lahira zai fi.

Hakanan manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam, ya taba tambayar Abuzar(RA) cewa, Abu Zar me kake tunani game da mutumin da yake da tarin Duniya, zaka kirashi me Arziki?

Abu Zar(RA) ya amsa da cewa, tabbas zan kirashi da me Arziki ya Rasulullah.

Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam ya sake tambayar Abu Zar, me zaka ce game da mutumin da bai da kudi, zaka kirashi matsiyaci?

Abu Zar(RA) ya amsa da cewa, zan kirashi da matsiyaci ya Rasulullah.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya sake tambayar Abuzar wadannan tambayoyi har sau 3, Abu Zar(RA) shima yana maimaita amsa kamar yanda ya bayar a farko.

Karanta Wannan  Addu'ar ciwon kirji

A karshe Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallam ya cewa Abu Zar(RA) wannan amsa taka ba daidai bace.

Ba haka ake gane me arziki ko matsiyaci ba. Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallam yace ba yawan tarin dukiya bane arziki, Arziki ko Talauci daga zuciyar mutum yake.

Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallam yace me wadatar zuci,Ghina, ko me ke faruwa a Duniya zai zama hankalinsa a kwance, ko da bashi da tarin Dukiya da kadarori.

Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallam ya kuma gayawa Abu Zar(RA) cewa, akwai kuma wanda be da wadatar zuci, To duk yawan dukiya da kadarorin da yake dashi zai rika ganin bashi da komai.

Domin samun wadatar zuci, Annabi Muhammad, Sallallahu Alaihi Wasallam ya bayyana Hadisil Qudsi, inda Allah yace, yaku bayina, ku ware lokaci daga cikin lokutanku dan Bautar Allah.

Allah yace idan kuka yi haka, zan cika zukatanku da wadatar zuci, watau Ghina, kuma zan kareku daga Talauci.

Allah Subhanahu wata’ala yace amma idan kuka ki yin hakan,  zan cika zukatanku da talauci.

Karanta Wannan  Addu’ar samun mijin aure da gaggawa

Watau anan zamu fahimci cewa, kiyaye Sallah, da sauran ibadoji da aka wajabta mana, yana jawowa mutum wadatar zuci, Arziki da kariya daga talauci.

Wuridin kudi nan take

Domin Samun kudi da gaggawa, ga abinda mutum ya kamata yayi.

Allah Subhanahu wata’ala ya fada mana cewa, Yaku wadanda suka yi imani, ku bayar(sadaka, kashe kudi ta hanyar daukaka kalmar Allah, ciyar da miskinai) daga abinda muka arzutaku dashi kamin rana ta zo wadda babu kasuwanci a cikinta, babu Abuta, babu ceto(sai da izinin Allah)(watau ranar Qiyama). Kuma masu kafurcewa sune Azzalumai.

al-Baqarah 2:254

Abu Huraira(RA) ya ruwaito Annabi Muhammad, Sallallahu Alaihi Wasallam yace, duk wanda ya bayar da sadaka daidai da dabino daya daga dukar halal da yake da ita, Allah baya karbar dukiyar haram sai me kyau, Allah zai karbi wannan sadaka ya sakata a hannun damarsa ya riritawa wanda ya bayar da sadakar, kamar yanda ake kula da jaririn doki har ya girma, har sai ta kai kaman girman babban dutse.

Karanta Wannan  Addu'ar Annabi Sulaiman

Al-Bukhaari, 1344; Muslim, 1014.

Abu Huraira(RA) ya sake ruwaitowa daga Annabi, Sallallahu Alaihi Wasallam yace, a kullun Allah yana saukar da mala’iku guda biyu, daya na addu’ar Allah ya nunkawa duk me bayar da dukiyarsa wajan ciyarwa, da taimako, dayan kuma yana addu’ar Allah ya lalata dukiyar duk wanda baya ciyarwa ya boye.

Al-Bukhaari, 1374; Muslim, 1010.

Kaga kuwa duk me ciyar da dukiyarsa komai kankantarta, yana samun addu’ar mala’ika ta cewa, Allah ya linka masa.

Abu Huraira(RA) ya sake ruwaito cewa, Annabi Muhammad, Sallallahu Alaihi Wasallam yace, Allah yace ku baiwa mutane dukiyarku, nima zan baku.

Al-Bukhaari, 5073; Muslim, 993.

Wuridin kudi: Wuridin kudi nan take

A takaice, idan mutum nason yayi kudi da gaggawa to ya kiyaye:

  • Yin Sallah akan Lokaci da cika sauran ibadu na farilla.
  • Bayar da sadaka.
  • Da Zikiri.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *