
Mutanen jihohin Katsina, Kano, da Jigawa na fuskantar matsi saboda karancin wutar lantarkin da suke samu inda a yanzu wutar awanni 2 kacal ake basu a yini.
Da yawan kananan ‘yan kasuwa sun koka da cewa suna fuskantar matsala wajan gudanar da ayyukansu saboda rashin ko karancin wutar a wadannan jihohi.
Yawancin kasuwancin da wannan matsala tafi shafa sune Teloli, Masu sayar da kankara, mas cajin waya, masu sana’ar walda da sauransu.
Hukumar wutar dake kula da wadannan jihohi, (KEDCO) ta bayyana cewa an samu karancin wutar ne saboda gyare-gyaren da take dan inganta ayyukanta.