Wednesday, January 15
Shadow

Ya ake gane cikin namiji

A yayin da kika dauki ciki zaki ta samun mutane suna miki magana da bayyana ra’ayoyinsu akan cewa, namiji ne kike dauke dashi ko mace.

Akwai dai maganganu na al’ada da camfe-camfe wanda a wannan rubutu zamu muku bayani dalla-dalla yanda lamarin yace a ilimance.

A ilimin likitanci, sun ce da zarar maniyyi ya shiga mahaifane ake tantance cewa namiji ne mace zata haifa ko mace.

Hakanan sunce kuma kalar ido, kalar gashi, da sauransu duk daga shigar maniyyi da kwan mace mahaifa duka ake tantancesu.

Al’aurar abinda ke cikinki zata fara bayyana ne a yayin da kika kai sati 11 da daukar ciki. Saidai duk da haka, ko da gwaji aka yi a wannan lokacin ba za’a iya tantance namiji ne zaki haifa ko mace ba.

Karanta Wannan  Cin yaji ga mai ciki

Maganganun da basu da inganci da ake amfani dasu wajan cewa kin dauki cikin mace ko namiji:

Zazzabin Safe: Ana cewa idan kina yawan yinshi, wai mace zaki haifa hakanan idan baki yawan yinshi, Namiji zaki Haifa.

Duka wannan babu gaskiya a cikin zancen.

A wani kaulin ana cewa idan mace zaki haifa, zaki rika yin kurage saboda zata kwace kyawunki, amma idan namiji ne ba zaki rika fama da kurajen ba.

Hakanan wai idan mace zaki haifa, gashin kanki zai rika zaizayewa saboda zata sace miki gashi, idan kuma namiji ne gashinki zai tsaya daidai.

Hakanan wai idan Mace zaki haifa zaki rika kwadayin kayan zaki irin su alewa, Yoghurt, da sauransu amma idan mace zaki haifa, zaki rika kwadayin kayan gishiri irin su Tsire, shinkafa da wake da sauransu.

Karanta Wannan  Siffofin mace mai ciki

Duka wadannan maganganu shaci fadi ne babu kanshin gaskiya a tattare dasu.

Hanyoyi ingantattu da ake gane jinsin abinda zaki haifa

Akwai gwajin Free cell DNA da ake yi yayin da kika kai sati 9 da daukar ciki.

Akwai kuma gwajin CVS da ake yi wanda shi kuma ana yinsa ne a yayin da kika kai sati 10 zuwa 12 da daukar ciki.

Akwai kuma gwajin Amniocentesis da ake yi yayin da kika kai sati 15 zuwa 18 da daukar ciki.

Saidai duka wadannan gwaje-gwaje suna da hadarin sawa a yi barin cikin.

Akwai na karshe, shine Gwajin Ultrasound wanda ake yi idan kika kai sati 18 zuwa 20 da daukar ciki.

Karanta Wannan  Yadda ake gwajin ciki da fitsari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *