MIYAR WAKE
Ingrediants :
1.Wake
2.Manja
3.Attarugu
4.Tattasai
5.Albasa
6.Tumatur
7.Maggi
8.Spices
9.Daddawa
10.Nama ko kifi
YADDA AKE HADAWA
Dafarko zaki jiya wakenki da ruwan zafi kibarshi yayi 30min sai ki surfashi aturmi ki wanke, kamar dai na alale.
Sai kisa waken atukunya tare da ruwa kidansa kanwa kadan sai ki daura akan murhu ki barshi ya dahu yayi luguf sai ki burgeshi.
Sai ki daura wata tukunya ki silala nama, sai ki soya manja sai ki zuba kayan miyan da kika jajjaga suma ki soyasu.
Sannan kixuba ruwan sulalen naman tare da naman ko kisa normal ruwa kibarshi ya tafasa sai kisa daddawa da spices dinki.
Kibarshi ya tafasa wato ya dahu kamar 30min sai ki dauko wannan waken da kika dafan sai ki juye acikin miyar kiburgesu.
Sai ki rege wuta kibarsu su dahu inya dahu zakiga manjan yayi yo sama.
Zaki iyaci da kowane irin tuwo.
Note : Zaki iya bayan kin surfa waken kin wanke sai ki markadashi kamar alale, bayan kin gama yin hadin miyar sai kisa markaden kibarshi ya nuna