Tuesday, March 18
Shadow

Ya kamata a jinjinawa Atiku Abubakar kan kokarin gyaran tattalin arzikin da yayi>>Inji El-Rufai

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ya kamata a jinjinawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kan kokarin gyaran tattalin arzikin da yayi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Ya bayyana hakane a wajan gaisuwar marigayi, Edwin Clark a jihar Delta.

El-Rufai yace yawanci mutane sun fi tunawa da abin ashsha da mutum ya aikata fiye da abin alkairi.

El-Rufai yace hadda shi sun yi aiki a karkashin Atiku suka gyara tattalin arzikin kasarnan a lokacin amma ba’a magana akan lamarin ko dan basu yi rubutu akan lamarin bane?

Karanta Wannan  Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *