
Tsohon Tsageran Naija Delta, Mujahid Asari Dokubo ya bayyana cewa, ya kamata a kama sojan ruwa, Yerima a hukuntashi biyo bayan abinda yawa Wike.
Asari Dokubo a sanarwar da ya fitar a wani Bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta yace ba wai yana goyon bayan Wike bane, yana goyon bayan gaskiyane.
Yace a Najeriya ne kadai irin haka zata faru kuma sojan yasha Lallai.