
Sanata Natasha Akpoti ta bayar da shawarar cewa, ya kamata a rika wa ‘yan majalisar Dattijai gwajin shan miyagun kwayoyi.
Ta bayyana hakane a matsayin martani ga sanata Sunday Karimi wanda shima dan jihar ta Kogi ne inda ya fito yana sukarta kan fadanta da sanata Godswill Akpabio.
Yace Natasha Akpoti ta jawowa jiharsu ta Kogi abin kunya sannan ta jawowa Najeriya ma abin kunya saboda abinda ta yi.
Yace fadan da sanata Natasha Akpoti ta yi da Godswill Akpabio ya nuna cewa, tsohon Gwamnansu na da gaskiya akan fadan da suka yi da sanata Natasha Akpoti.
A baya dai, tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello sun sha dambarwa da Sanata Natasha Akpoti.
Sanata Sunday yace sun yi kokarin baiwa Sanata Natasha Akpoti baki amma taki fahintarsu.