
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, babu dan siyasar da ‘yan Adawa zasu hada kai su taso suna son kayar dashi mulki kamar yanda ake masa, amma yayi shiru yaki yin magana.
Shugaban ya jawo hankalin ‘yan Najeriya da cewa su daina baiwa ‘yan siyasar dake son kayar dashi zabe a 2027 muhimmanci.
Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai jihar Nasarawa inda ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ta gudanar.