Babban lauya kuma me ikirarin kare hakkin bil’adama, Femi Falana ya nemi majalisar tarayya data gaggauta amincewa da kudirin dokar da zai karawa ma’aikata mafi karancin Albashi kamar yanda ta yi akan kudirin dokar canja taken Najeriya.
Falana a wata sanarwa da ya fitar yace, tsohuwar dokar kudirin mafi karancin Albashi ta daina aiki dan haka akwai bukatar majalisar ta amince da sabuwar kudirin dokar.
Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dai sun fara yajin aiki a yau, Litinin dan nuna kin amincewa da karin Naira dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi.
Wannan kira na Femi Fala dai zai yiwa ma’aikata da yawa dadi ganin cewa hakan zai kawo fara biyan sabon mafi karancin Albashin da gaggawa.