
Kungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihohin Arewa 19 da Abuja ta bayyana rashin jin dadinta kan yanda ake samun wasu suna batawa dan shugaban kasa, Seyi Tinubu suna da yada karya akansa.
Shugaban kungiyar, John Joseph Hayab ne ya bayyana hakan inda yace mutane su sani akwai rayuwa bayan mahaifinsa, Tinubu ya sauka daga shugaban kasa.
Ya kara da cewa, yada karya ya sabawa Al’ada da Addinin da muke bi.
Yace dan haka kamata yayi kafafen watsa labarai su rika tantance labari kamin su yadashi.