Wednesday, November 12
Shadow

Gwamnan jihar Rivers da Tinubu ya dakatar, Fubara ya je gidan Wike dan neman a sasanta, ji yanda ya kwanta kasa yana rokon Wike

Rahotanni sun bayyana cewa, dakataccen gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya je gidan ministan Abuja, Nyesome Wike dan neman a sasanta.

Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Fubara ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a birnin Landan.

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun da tsohon gwamnan jihar, Olusegun Osoba ne suka yiwa Fubara jagoranci zuwa gidan Wike.

Rahoton yace Fubara ya kwanta kasa ya gaishe da Wike inda ya rika kiransa da Ogana Ogana. Wata majiya tace sai can duhu yayi sosai sannan Fubara ya bar gidan.

Hakanan majiyar ta kara da cewa, Wike ya bukaci Fubara ya je ya tara mutanensa ya gaya musu ainahin abinda ya hadasu fada.

Karanta Wannan  Ina godiya ga Likitocin da suka min aikin kara girman Nònùwà da mazunai>>Inji Dan Daudu, Bobrisky, kalli Sabon Hoton da ya saki da mutane ke cewa tabbas ya koma mace sak

Kakakin Wike, Lere Olayinka ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayanin abinda ya faru ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *