AWARA A SAUKAKE
A tsince waken suya akai Nika aniko a tace da abun Tata a daura kanwuta inya tafaso a zuba ruwa lemon Sami harya taso sama, ana iya samun kwano a matse lemun tsamin a ciki a dan kara ruwa sai a rika zubawa kadan-kadan, za’a ga kumfan waran ya taso sama.
Sai A tsame a zuba abin Tata irin na tatar koko amatse ruwan dake jiki, wasu na dora turmu akai,ko dutse dan ruwan ya fita sosai, idan ruwan ya gama fita sai a dora a faranti ko wani abu me fadi ayanyanka.
Sai a zuba mar jajjagen attarugu da Albasa da tafarnuwa da gurjejjen karas Sai curry da maggi
Idan ana so za’a iya saka kwai amma ba dole bane
Sai a saka a mai a soya.
Akwai Dadi sosai