Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake dafa taliya da makaroni

Ana dafa Taliya da makaroni a cisu da miya, ko a yi Jollof dinsu ko a ci da mai da ya ji da dai sauransu, ya danganta da bukatar da ake da ita.

Yanda ake dafa Taliya da makaroni fari shine:

A samu tukunya me kyau a zuba ruwa kofi 4 ko 5 a barshi ya tafasa.

Bayan ya tafasa sai a zuba Taliya da makaronin a lokaci guda.

A barsu su dahu zuwa minti 15 ko 20.

Sai a sauke a tace ko kuma idan ruwan ya tsotse sai a sauke kawai a ci da abinda ake so.

Idan kuma Jollof za’a yi.

Sai a tanadi kayan Miya na leda ko danye a markadashi.

A tanadi Magi.

Karanta Wannan  Yadda ake miyar kuka

A tanadi man ja ko man gyada ya danganta wanda ake so.

A tanadi Kifi ko nama, ko kashin miya, ya danganta wanda aka fi so.

A tanadi Albasa.

A dora Tukunya a wuta a zuba man ja ko man kyada. A zuba kifi ko naman da aka tanada a yanka Albasa a ciki.

A soya sosai, idan suka soyu sai a zuba kayan miyan da aka tanada, su soyu zuwa mintuna 5 haka sai a zuba ruwa kofi 4.

Idan kuma kashin miyane za’a yi amfani dashi.

Bayan a zuba man a cikin tukunya, sai a yanka albasa, idan ta yi ja sai a zuba kayan miyan su soyu zuwa mintuna 5 haka, sai a zuba ruwa kofi 4 tare da kashin miyar.

Karanta Wannan  Yadda ake wainar gero

A barsu sai ruwan ya tafasa sosai, musamman idan da kashin miya ake amfani a bari ruwan ya tafasa sosai, sai a zuba taliya da makaroni a lokaci guda.

Bayan mintuna 15, sai a zuba magi a yanka albasa da curry, da karas idan da hali sai a juya, sai a rage wuta a barshi zuwa mintuna 5 sai a sauke a ci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *