Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake dafa taliya da wake

Taliya da wake na daya daga cikin abincin da mutanen kasar Hausa ke son ci, ga bayanin yanda ake dafata kamar haka:

Da farko dai bari mu yi bayanin yanda aKe dafa Taliya da wake fara wadda za’a iya ci da miya ko wani abu daban.

Zamu yi bayanin dafa taliya leda daya da wake kofi daya:

Za’a samu wankakkiyar Tukunya a zuba ruwa kofi 4.

Bayan ya tafasa, sai a wanke waken a zubashi a cikin ruwan, a barshi ya kai akalla mintuna 15 zuwa 20, sannan sai a zuba taliyar.

Idan An zuba taliyar a juyasu dan su hade amma ba sosai ba dan kada ya dame.

Karanta Wannan  Yadda ake wainar shinkafa

A barsu su dahu zuwa minti 15 ko 20 sai a sauke. Idan da sauran ruwa a tace idan babu shikenan.

Za’a iya cin ta da miya ko ganye ko wani Abu daban:

Yadda ake dafa taliya da wake dafaduka ko Jollof

Idan kuwa Jollof din Taliya da wakene za’a dafa, to ga yanda za’a dafata.

A samu wankakkiyar Tukunya a zuba man ja ko farin mai, ya danganta wanda ake son yin abincin dashi a dora a wuta, a dan yanka Albasa.

Idan da hali a saka kifi ko nama a cikin man a soya su tare.

Ko kuma za’a iya bari sai an gama soya man an zuba kayan miya, an zuba ruwa sai a saka naman ko kashi a cikin ruwa ya tafasa tare da ruwan.

Karanta Wannan  Yadda ake yin pizza

Idan soya naman aka yi ko kifin, bayan ya soyu, sai a zuba jajjagen kayan miya ko kuma na leda wanda aka siyo ko wanda aka yi grating a dan soya zuwa minti 2 ko 3 haka.

Sannan sai a zuba ruwa kofi 4, a barshi ya tafasa. Anan ne za’a zuba nama ko kifi idan ba’a soyashi tare da man a farko ba.

Bayan ya tafasa sai a zuba waken kofi daya da aka wanke. A barshi ya dahu zuwa minti 15 ko 20. Daganan sai a zuba taliyar itama.

A barsu su dahu zuwa minti 15 ko 20 haka.

A yayin da ake jiran dahuwar su, a tanadi magi(anan muna maganar magi dunkule, irin su me star, Dangote da sauransu) a yayyanka Albasa, idan so samu ne a sa me lawashi, idan da hali a samo karas shima a yanka a ajiye.

Karanta Wannan  Yadda ake zobo mai dadi

Idan Taliyar da waken suka kai mintuna 15 zuwa 20 a wuta, sai a dakko wannan magin da aka ajiye kamar guda 5 zuwa 7 a marmashe su a ciki, sannan a zuba wannan albasar da karas din a juya sosai su gauraye ko ina.

Sai a rage wuta a rufe abincin zuwa mintuna 5 haka.

Bayan nan sai a sauke, abincin ya dahu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *