Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake dambun kifi

YADDA AKE DAMBUN KIFI

Kayan hadi

– Kifi

– Attarugu

– Albasa

– Tafarnuwa

– Sinadarin dandano

– Garin curry

– Gishiri

– Man gyada

Yadda ake hadawa

– A wanke kifin a gyara shi sosai, sai a dora tukunya a kan wuta, a zuba kifin da kayan kamshi da kayan dandano da tafarnuwa da sauransu.

– A zuba ruwa kadan sai a bar shi ya dan dahu kadan, sai a sauke.

– A kwashe ya sha iska sai a saka a turmi a daka shi har sai ya daku yadda ake so, a kwashe a ajiye a gefe.

– Sai a daka attarugu da albasa a hada da kifin a gauraya sosai.

– Zuba sinadarin dandano da garin curry a ciki sai a jujjuya su hadu sosai.

Karanta Wannan  Duk inda kuka ga banza ta fadi, zaku ci abinci kyauta, kada ku yi wasa da wannan damar ku ci>>Kakakin Majalisar Dattijai, Godswill Kapadia ya baiwa 'yan Najeriya shawara

– A dora tukunya a wuta sai a zuba man gyada kadan a soya yadda ake so.

Shi ke nan sai ci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *