Canjin kalar fitsarin mace me ciki abune wanda ba bako ba.
Idan mace me ciki ta yi fitsari, idan aka duba za’a ga fitsarin ya kara duhu fiye da a baya.
Wannan canjin kala na fitsari a mafi yawan lokuta ba matsala bane. Saidai a wasu lokutan da basu cika faruwa ba, yakan iya zama matsala.
Yawanci kalar fitsari ruwa dorawa ne watau Yellow wanda bai ciza ba, amma na me ciki za’a ga yayi Yellow ko ruwan dorawa sosai.
Hakanan zai iya zama kalar Mangwaro.
Dalilan dake kawo Canjawar kalar Fitsarin mace mw ciki:
Rashin isashshen ruwa a jiki:
Cutar Infection a mafitsara.
Cutar mafitsara da ake cewa, UTI.
Canja kalar abincin da ake ci lokacin daukar ciki.
Magungunan da ake sha lokacin da ake da ciki.
Fitsari da jini, watau tsargiya.
Cutar koda ko wani abu makamancin haka.
Wadannan abubuwan da muka jero sune ke kawo canjawar kalar fitsari lokacin da mace ke dauke da ciki.
Saidai canjin mafi yawanci na dan lokacine, ba ya dawwa ma, kuma bai cika cutarwa ba.
Amma idan ya dade kuma aka shiga damuwa, ana iya tuntubar likita.