Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake tuwon madara

TUWON MADARA

INGREDIENTS:
1.Madaran gari rabin loka
2.Sugar gwangwani biyu

  1. Leda

PROCEDURE: A samu ruwa kamar rabin kofi a zuba a tukunya sai a juye sugar, a barshi yayi ta dahuwa har sai yayi kauri. In kika dangwala zaki ga yana yin ďanko kamar na aya mai sugar.

Sai ki ďauko madarar kina juya wa kina zubawa, idan ya shige duka shikenan in kuma bai shige ba sai ki bar sauran. Amma kada yayi qarfi sosai kada ki ce dole sai duka madarar ki ta shige.

Sai a juya bayan tray a shimfida leda a kwashe kafin ya fara yin brown, kada kice zaki barshi bayan kin juya, yana hade wa ki sauke. A samu mara ko muciya (kneading stick) a sa shi yayi plat dai-dai kauri ko faďin da kike so. Shikenan sai a yayyanka shape ďin da ake so.

Karanta Wannan  Yadda ake miyar kuka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *