Wednesday, January 15
Shadow

Yadda mace zata gane ta rasa budurcinta

Rasa budurci zai iya zama ta hanyar yin jima’i ko ba ta hanyar jima’i ba.

Dan mace bata taba yin jima’i ba hakan ba yana nufin har yanzu budurcinta na nan ba, tana ina rasa budurcinta ta hanyar yin aikin karfi ko kuma tura wani abu cikin farjinta.

Likitoci sun ce wasu matan ma ba’a haihuwarsu da marfin farji wanda ake cewa budurci.

Sannan idan mace ta rasa budurcinta za’a iya ganin jini kadan a gabanta.

Saida ba kowace macce ke ganin jini bayan rasa budurci ba.

Idan kuwa ta hanyar jima’i ne, ba lallaine mace ta ji zafi ba, ya danganta, misali idan Amaryace, ya kamata mijinta ya yi kokarin su yi wasa sosai dan gabanta ya kawo ruwa ta yanda idan suka fara jima’i ba zata ji zafi ba.

Karanta Wannan  Maganin dawo da budurci

Hakanan idan amarya ya kasance ta fara jin zafi, ya kamata a dakata.

Ana iya amfani da baby oil, man zaitun, ko man kwakwa dan shafawa a gaban amarya dan kada ta ji zafi yayin jima’i.

Hakanan fatar budurci dake tarw gaban mace ba lallaine ta yage ba bayan an yi jima’i a karin farko ba, kuma yana iya yiyuwa ta yage kamin yin jima’i ta hanyoyi daban-daban kamar yanda muka bayyana a sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *