Friday, December 5
Shadow

Yaduwar Gurbatacciyar Shinakafa me kisa a Najeriya ta saka fargaba

Hankula sun tashi a jihohin Ogun da Legas saboda farfagandar yaduwar shinkafa me guba dake kisa.

‘Yan uwa da dangi sun rika aikawa jina sakonni musamman ta WhatsApp inda ake gargadinsu da cin shinkafa, ana yada cewa, wata mata ce ‘yar kasuwa aka kwacewa Shinkafar aka shigo da ita Najeriya inda ita kuma ta yi tsafi kan duk wanda ya ci ya mutu.

Rahoton yace masu yada wannan labari sunce har wasu sojoji da jami’an Kwastam sun rasu sanadiyyar wannan shinakafa, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Hakanan rahoton yayi ikirarin cewa, Mutane 70 sun mutu sanadiyyar shinkafar.

Iyaye har makaranta sun rika bin ‘ya’yansu suna gargadin masu abinci kada su sayarwa da ‘ya’yansu Abinci.

Karanta Wannan  Da Duminsa:Duk da cire gwamna Fubara da Jibge jami'an tsaro, Tsageran Niger Delta sun sake fasa butun gas a jihar Rivers

Saidai Tunu hukumomin Kwastam na jihohin Ogun da Legas suka musanta wannan zargi.

Sun ce babu wata shinkafa me guba da aka shigo da ita Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *