Yahaya Bello ya buƙaci ƴan Nijeriya da su taimaka wa Tinubu da addu’a
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya roki ƴan Najeriya da su yi hakuri da shugaban kasa Bola Tinubu, tare da tallafa masa da addu’o’i domin samun nasara a kan manufofinsa na gyaran tattalin arzikin ƙasa.
Bello ya yi wannan jawabi ne a jiya Talata a fadar Ohinoyi na Ebiraland da ke Okene, inda ita ce fitar shi ta farko a bainar jama’a tun bayan da ya samu ’yancinsa daga gidan yari, inda bayan da koru ta bayar da belinsa a gaban kotu bisa tuhumarsa da laifin karkatar nlda N110bn.
Tsohon gwamnan wanda ya samu tarba daga dimbin magoya bayansa a yankin Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ya yi kira da bukatar hadin kai da hakuri da shugaban ƙasa.
Bello, wanda ke tare da magajinsa, Gwamna Usman Ododo, ya ce, “Gwamnatin Shugaba Tinubu na bukatar lokaci domin tunkarar kalubalen da ke shafar ci gaban Najeriya, kuma dole ne ƴan Najeriya su ci gaba da yi masa addu’ar samun nasara.