
Kungiyar kwadago ta TUC ta jadada cewa, babu gudu ba ja da baya akan maganar yajin aikin da take shirin yi dan nuna rashin jin dadin karin kudin kiran waya dana data.
Shugaban kungiyar, Festus Osifo ne ya bayyana haka a ganawar da aka yi dashi a ChannelsTV.
Yace abinda ya kawo tsadar kudin gudanarwa na kamfanonin sadarwar, farashin canjin kudin Naira da dala ne wanda kuma gwamnati zata iya yin maganinsu.
Yace gwamnati ce ke da alhakin magance matsalar ta kamfanonin sadarwar ba wai su rika fanshewa akan talakawa ba.