Wednesday, January 15
Shadow

‘Yan Banga a jihar Naija sun yi nasarar kashe ‘Yan Boko Haram da dama

Zaratan ‘yan Banga a garin Alawan da Bassa dake jihar Naija sun yi nasarar kashe ‘yan Boko Haram da dama.

Rahoton da hutudole ya samu daga wata majiya dake yankin ya bayyana cewa lamarin ya faru sa sanyin safiyar ranar Laraba.

‘Yan bangan sun kashe da dama daga cikin maharan inda suka kama wasu da ransu.

Hutudole ya ga gawarwakin ‘yan Boko Haram din amma saboda muninsu yasa ba zamu iya wallafasu anan ba.

Maharan dai su 20 ne inda auka yi nasarar kashe mutane 2 da harbin mutum daya hakanan a cikin ‘yan bangar ma, an kasheutane biyu.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya Ta Tara Naira Bilyan 60 Daga Cire Tallafin Taki, Inji Hukumar NSIA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *