Ayaba na daya daga cikin kayan itatuwan da ake ci amma amfaninta ba ga ci a ciki a koshi bane kawai, tana kuma da amfani wajan gyaran jiki, musamman fuska.
Daya daga cikin Amfanin Ayaba a fuska shine, musamman wadanda suka fara manyanta, fuska ta fara tattarewa, Ayaba na taimakawa matuka wajan gyara tattarar fuska wandda ke zuwa sanadin tsufa.
Hakanan tana yakar abubuwan da ake kira da Free Radicals wanda sune ke saurin kawo tsufa ga fata.
Ayaba tana taimakaaa matuka wajan boye kurajen fuska, amfani da ita a fuska yana kwantar da kumburin kuragen fuska ya zamana kamar babusu.
Hakanan Ayaba tana boye tabon fuska da shacin rana da yakewa fuska.
Hakanan tana baiwa fatar jiki kariya daga duhun zafin rana, ma’ana idan aka shafata aka shiga rana, zafin ranar ba zai cutar ba.
Hakanan ga masu fama da bushewar fuska, Ayaba na taimakawa wajan saka fuska ta rika maski.
Saidai Wasu mutanen Azayaba na musu side effects ko ace illa idan suka yi amfani da ita, illolin da takan yi sun hada da:
Yawan Atishawa.
Kaikayi
Kumburi.
Da sauransu,idan aka gwada aka ga wannan illa, to a daina a nemi wata hanyar gyaran fuska dan kada a cutu.
Yanda ake amfani da Ayaba dan Gyaran Fuska:
Ana samun ayaba wadda ta nuna a markada ta ko a kada ta ta zama ta hade waje guda ta yi kamar kunu ko a yi blending dinta, ana iya amfani da hannu.
Wasu na amfani da bawon ayaba su goga a fuska amma hakan bai cika bada sakamakon da ake so ba.
Ana hada ayaba da zuma a shafa a fuska dan maganin kurajen fuska, da maganin bushewar Fuska.
Ana hada ta da kasa me kalar ja, wadda ake cewa Clay a turance, wannan hadi yana maganin yawan mai a fuska da kuma tsaftace fuskar sosai.
Ana hada ayaba da ruwan lemun tsami ko lemun zaki dan kadan, wannan hadi yana batar da tabon fuska.
Ana hadata da Avocado a nika ko a markada ko a dama dan samun fuska me sheki.
Ana hadata da Yegot a dama a shafa a fuska dan samun fuska me sheki.
Ana hada ayaba da Tumeric ko kurkur a dama dan maganin kurajen fuska da tabon fuska,kuma wannan hadi yana kara hasken fuska.
Ya danganta da irin hadin da ake son a yi, a hada kayan hadin a dama da hannu ko da wani icce ko ludayi ana iya saka ruwa idan ana da bukatar hakan.
Sai a shafa a fuska, a bari ya kai mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi.
A goge fuskar sai a shafa mai.
Domin samun sakamako me kyau, a maimaita sau 2 zuwa 3 a sati.