
‘Yan Bìndìgà a jihar Katsina sun kashe wani babban malamin Addinin Islama me suna Sheikh Mustapha Aliyu Unguwar Mai Kawo.
‘Yan Bindigar dai sun yi garkuwa dashi inda suka ajiyeshi a wajensu na tsawon sati 3.
Malamin shine shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam ta karamar hukumar Kankara.
Kuma an yi garkuwa dashi ne a garinsu na Unguwar Mai Kawo wanda hakan ke kara bayyana matsalar tsaron da ake fama da ita.
Bakatsinene ya bayyana rasuwar tasa da yammacin Ranar Juma’a.