Sunday, November 16
Shadow

‘Yan Bindiga sun kàshè shahararren malamin Addinin Islama a jihar Katsina bayan sun yi garkuwa dashi

‘Yan Bìndìgà a jihar Katsina sun kashe wani babban malamin Addinin Islama me suna Sheikh Mustapha Aliyu Unguwar Mai Kawo.

‘Yan Bindigar dai sun yi garkuwa dashi inda suka ajiyeshi a wajensu na tsawon sati 3.

Malamin shine shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam ta karamar hukumar Kankara.

Kuma an yi garkuwa dashi ne a garinsu na Unguwar Mai Kawo wanda hakan ke kara bayyana matsalar tsaron da ake fama da ita.

Bakatsinene ya bayyana rasuwar tasa da yammacin Ranar Juma’a.

Karanta Wannan  ABIN A YABA: Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A Jihar Neja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *