
‘Yan Bindiga a jihar Zamfara sun kakabawa kauyuka 12 harajin Naira Miliyan 60 saboda sunce mutanen wadannan kauyukan sun baiwa jami’an tsaro bayanan sirri da suka kai ga kai musu hari da tarwatsa su.
Garuruwan da ‘yan Bindigar suka sakawa wannan harajin sun hada da Koloma, Dan Hayin Zargado, Zargado, Dan Godabe, Sabuwar Tunga, Makini, Bubaka, Yelwa, Bahwada, Koda, Manya, da Kabusu.
Mutanen kauyen sun bayyana cewa idan suka sake basu biya wannan haraji ba, ‘yan Bindigar zasu afka musu da kisa da garkuwa da kona musu gidaje.
Bakatsine ne ya bayyana hakan a shafinsa na X inda yace idan ba’a dauki mataki ba, komai na iya faruwa.
Tsohon Kansilan Dankurmi, Hon. Iliyasu Salisu Dankurmi ma ya tabbatar da hakan a hirar da BBChausa ta yi dashi.