Kwamishinan ‘yansandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalinja ya tabbatar da mutuwar ‘yansanda 5 da sojoji 2 wanda ‘yan Bindiga suka kashe a karamar hukumar Tsafe dake jihar.
Ya bayyana cewa ‘yan Bindigar sun yiwa jami’an tsaron kwantan baunane inda suka bude musu wuta a kan hanyar Gusau zuwa Funtua ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa, ‘yan Bindigar sun tafi kaiwa kamfanin gini na Setraco Company Hari ne inda jami’an tsaron suka samu bayanan sirri suka tafi dan taresu.
Yace yanda aka yi suka kashe musu jami’ai kenan.