Masu garkuwa da mutane sun sace sojojin Najariya 3 da wasu farar hula a Enugu, lamarin ya farune ranar Alhamis, 9 ga watan Janairu a hanyar Enugu zuwa Nsukkah.
Motocin haya na bas 3 ne ‘yan Bindigar suka tare inda da farko suka yi garkuwa da sojoji 4 amma daga baya daya ya tsere.
Sojan da ya tsere din shine PTE Usendu Emediong (24NA/87/7560) amma sauran ukun, PTE Usoro Ezekiel Paul (24NA/87/6751), Jeremiah Inimbom Thomas (24NA/87/7937) da PTE Victor Itiat Godwin (24NA/87/8348) an yi garkuwa dasu tare da sauran fasinjojin.
Wani shaida yace maharan sun kwashe kusan awa daya suna tare da hanyar kamin daga baya su tasa keyar wadanda suka yi garkuwa dasu zuwa cikin daji a kafa.
Rahoton yace jimullar mutane 35 ne aka yi garkuwa dasu.