
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan Bindiga sun yi garkuwa da wannan matashiyar ‘yar bautar me suna Rofiat Lawal.
Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da itane akan titin Benin-Ore yayin da take dawowa daga Benin dan zuwa inda aka turata aiki.
Rahoton yace wanda suka yi garkuwa da ita na neman Naira Miliyan 20 a matsayin kudin fansa kamin su saketa.
Shugaban masu bautar kasa na jihar Oyo, Odoba Oche ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun sanar da jami’an tsaro sannan yace bai san ko an nemi kudin fansa ba.