Monday, January 27
Shadow

‘Yan kasuwar man fetur zasu daina sayen man fetur din daga matatar man Dangote inda zasu koma shigo dashi daga kasar waje saboda yafi Arha

Yan kasuwar man fetur zasu daina sayen man fetur daga matatar man fetur ta Dangote inda zasu rika shigo dashi daga kasashen waje saboda na kasar wajen ya fi arha.

Rahotanni sun bayyana cewa idan ‘yan kasuwar suka shigo da man fetur din daga kasar waje har ya zo Najeriya zai zo musu ne akan farashin Naira N922.65 akan kowace lita, wannan farashin ya hada da duka farashin jirgin ruwa da ya dakko man fetur din da canjin dala da aka yi da kudin haraji da komai da komai.

Saidai idan kuma zasu sayi man a hannun matatar man Dangote zasu sayeshi ne akan farashin Naira N955 akan kowace lita.

Karanta Wannan  Duk da ciyo bashin Dala Biliyan $3.2 Najeriya ta kasa samar da ingantacciyar wutar Lantarki

Hakan yana nufin sun samu saukin Naira N32.35 idan suka sayi man fetur din daga kasashen waje maimakon matatar man fetur ta Dangote.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da bai so a bayyana sunansa ya bayyanawa jaridar Punchng cewa, dolene da yawan ‘yan kasuwar su koma sayen man fetur din daga kasashen waje saboda saukin da zasu samu.

A ranar Lahadin data gabata, matatar man Dangote ta bayyana kara farashin man fetur din daga Naira N899.50 da aka saba saye inda tace karin dolene saboda kara farashin danyen man fetur da aka samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *