
Gwamnatin tarayya ta koka da cewa, ‘Yan kwaya sun karu a Najeriya.
Hakan na zuwane yayin da ake tunawa da zagayowar ranar yaki da shan kwaya da safararta a Duniya.
Gwamnatin ta yi kiran hada kai dan yakar wannan matsala.
Babbar sakatariya a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Daju Kachollom, cee ta bayyana hakan a ganawa da manema labarai.
Tace matsalar ta’ammuli da miyagun kwayoyi ba matsalar mutum daya bace ko kuma masu sha kawai, matsala ce ta kowa da kowa dan haka hadin kai wajan magance matsalar ke da muhimmanci.