Friday, December 5
Shadow

‘Yan majalisa sun tambayi ministan kudi Wale Edun ya gaya musu yanda aka yi da kudin tallafin man fetur da aka cire, saidai yace ba zai fada ba a gaban ‘yan jarida saidai a sirri

Kwamitin Majalisar dattijai dake saka ido kan yanda ake kashe kudaden gwamnati ya nemi ministan kudi, Wale Edun yayi bayani kan yanda aka kashe kudin tallafin man fetur da aka cire.

Saidai Wale yace wannan magana ta sirri ce, dan haka ne kwamitin suka kori ‘yan majalisa daga zaman dan Wale ya musu bayani.

Wannan magana ta taso ne bayan da sanata Senator Abdul Ningi dan PDP daga jihar Bauchi ya bukaci hakan.

Shugaban kwamitin, Senator Olamilekan Adeola ya nemi ‘yan jarida su fita daga zaman dan a samu a yi maganar yanda aka kashe kudin tallafin man fetur da aka cire.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Wani Matashi Daga Jihar Adamawa Ya Fara Tattaki Zuwa Katsina domin nuna goyon bayansa ga mawaki Dauda Kahutu Rarara, da kuma halartar gaisuwar rashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a garin Daura

Gwamnatin tarayya dai tace ta cire tallafin man fetur ne dan amfani da kudaden wajan yin ayyukan raya kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *