
‘Yan majalisar Dattijai sun tafi hutun watanni biyu da suka saba yi duk shekara.
Sai nan da watan Satumba 23 sannan zasu dawo daga hutun.
Saidai kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, sauran kwamitin majalisar zasu ci gaba da aiki a yayin da ake hutun.