‘Yan majalisar tarayya dake jam’iyyun Adawa irin su PDP, Labour party da sauransu, sun yi kiran cewa, ya kamata gwamnati ta biya ma’aikata Naira dubu 100 a matsayin mafi karancin Albashi.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Punch.
Yace a halin da ake yanzu, duk albashin da za’a biya dake kasa da Naira 298,000 ba zai kai ma’aikaci ko ina ba.
Ya kara da cewa, kasa biyan albashin da zai ishi ma’ikata yin rayuwa me kyau, sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ne.