Saturday, January 3
Shadow

‘Yan Najeriya miliyan 2 ne ke fama da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki: Karanta Jadawalin Jihohin da suka fi yawan masu cutar a Najeriya

Jihohi 3 ne suka fi yawan masu dauke da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki a Najeriya.

Jihohin sune Rivers, Benue, and Akwa Ibom, hakan ya bayyana ne daga hukumar dake kula da cutar ta kasa.

Rahoton yace mutane sama da miliyan 2 ne ke fama da cutar a Najeriya.

Jihohin dake da yawan mutane masu cutar sune kamar haka:

Rivers nada mutane 208,767

Benue na da mutane 202,346

Jihar Akwa Ibom na da mutane 161,597

Jihar Legas na da mutane 108,649

Jihar Anambra na da mutane 100,429

Sai Abuja dake da mutane 83,333

Delta na da mutane (68,170)

Imo na da mutane (67,944)

Karanta Wannan  Na kusa da Shugaba Tinubu kakkangeshi suke, basa bari a je kusa dashi ballantana a gaya masa halin da mutane ke ciki, watanni na 18 ina aiki a fadar shugaban kasa amma sau 3 muka taba haduwa da shugaban kasa shima a masallaci ne>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad

Enugu na da mutane (61,028)

Edo na da mutane (60,095)

Taraba na da mutane (58,460)

abia na da mutane (54,655)

Kaduna na da mutane (54,458)

Kano na da mutane (53,972)

Jihar Filato na da mutane 51,736

Borno na da mutane (50,433)

Hutudole.com ya ci gaba da kawo muku cewa jihar Oyo na da mutane (50,063)

Sai Cross River na da mutane (43,452)

Jihar Ogun na da mutane (43,348)

Sai Nasarawa na da mutane (44,993)

Hutudole ya fahimci jihar Adamawa na da mutane 40,059

Sai Gombe na da mutane (31,825)

Jihar Jigawa na da mutane (31,409)

Osun na da mutane (30,714)

Karanta Wannan  Matatar man fetur ta Dangote tasa matatun man kasashen Turai dole suna kullewa saboda kasashen Afrika sun daina sayen man su, na Dangote suke saye

Jihar naija na da mutane (29,756)

Hutudole ya ruwaito jihar Kwara na da mutane (20,259)

Sai Kebbi na da mutane (19,339)

Jihar Ekiti na da mutane (18,857)

Sai Sokoto na da mutane (15,223)

Jihar Ebonyi na da mutane (14,151)

Sai Zamfara na da mutane (13,253)

Hutudole ya fahimci jihar Kebbi ce me mutane mafiya karanci masu dauke da cutar Kanjamau din a Najeriya inda take da mutane (11,956)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *