Wednesday, September 2
Shadow

Karya ake mana, bamu ce muna goyon bayan Peter Obi da El-Rufai su yi takarar shugaban kasa a shekarar 2027 ba>>Inji Gwamnonin PDP

Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun musanta jita-jitar da ke cewa wasu daga cikinsu Guda biyar na Goyon bayan tikitin El-Rufai/Obi a zaɓen 2027.

Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Dakta Emmanuel Agbo, ya fitar a madadinsa a yau Asabar.

Ya ce, “Wajibi ne a gare mu a matsayin ƙungiyar Gwamnonin PDP, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, mu fito mu karyata, kuma mu yi Allah-wadai da wadannan jita-jita marasa tushe da wasu ‘yan siyasa masu son zuciya ke yayatawa. Su ne dai ba za su iya jure irin kokarin da muke yi don nuna gazawarsu a shugabanci ba, wanda ya jefa ‘yan Najeriya cikin fatara da tsananin wahala.”

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo; Saheer Abdul yayi karin haske kan labaran da ake yadawa cewa yana da mata 7

“A saboda haka, ƙungiyar gwamnonin PDP ba ta da wata alaka da waɗannan mutane, kuma ba ta da wani shiri na goyon bayan wata yarjejeniya da wasu ke ƙoƙarin yi a bayan fage don marawa tikitin Nasir El-Rufai/Peter Obi baya a zaɓen 2027.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *