Jam’iyyar Labour party ta bayyana cewa ta na da karbuwa a wajan talakawa ta yanda ko da bata hade da kowace Jam’iyya ba zata iya yin nasara a zaben shekarar 2027.
Jam’iyyar tace irin nasarar data samu a shekarar 2023 alamace dake nuna cewa zata iya yin nasara a zaben me zuwa ba tare da hadaka da kowa ba.
Sakataren yada labarai na Jam’iyyar, Obiora Ifoh ne ya bayyana haka a ganawarsa da jaridar Punchng.
Yace babu wata yarjejeniyar hadaka tsakanin Jam’iyyarsu da NNPP ta Kwankwaso ko PDP ta Atiku.
Ya kara da cewa babu wanda ya gayyacesu dan yin wata maganar hadaka.
A baya dai, shima Kwankwaso ya musanta cewa sun yi hadaka da Atiku dan tunkarar zaben shekarar 2027.