
Rahotanni daga hukumar kula da wutar Lantarki ta kasa,NERC sun bayyana cewa, ‘yan Najeriya sun biya jimullar Naira Tiriliyan 1.13 a matsayin kudin wutar a cikin watanni 6 da suka gabata.
Hakan na zuwane duk da kukan rashin wutar da ‘yan Najeriyar ke yi.
A shekarar data gabata dai Wutar Lantarkin Najeriya ta samu tangarda sosai.
Kuma Gwamnatin ta bayyana cewa kudin tallafin wutar da take bayarwa sun haura Tiriliyan 2.