
Danmajalisar da wakiltar mazaɓar Ɓagwai da Shanono a Majalsar Wakilan Najeriya ya nemi ƙarin jami’an tsaro sakamakon abin da ya kira hare-haren ‘yanfashin daji a yankin.
Yusuf Badau ya yi kiran ne yayin wani ƙudiri da ya gabatar a gaban zauren majalisar yau Talata, inda ya lissafa lokutan da aka kai musu wasu hare-haren.
“Yan bindigar sun fara kai hari ne wata kasuwa da ke garin Farin Ruwa a ƙaramar hukumar Shanono ranar 17 ga watan Afrilu, inda suka kashe mutum biyu, da raunata mutum shida kuma suka sace mutum ɗaya,” in ji shi.
“Sun sake kai irin wannan hari a garin Shanono ranar 26 ga watan Afrilun, sai dai mutanen garin sun tari ƴanbindigar kuma suka kore su.
“A ranar 2 ga watan Mayu a garin Fafarawa da Sandamu na Shanono da Bagwai, sun yi garkuwa da mutum daya da sace wayoyi, da babura bakwai, sai dai ba a samu asarar rayuka ba.”
Majalisar ta aika batun kwamitin majalisar na tsaro da yansanda don daukar mataki na gaba.