Thursday, April 2
Shadow

Yanda jigon jam’iyyar APC daga jihar Kano ya rasu a Otal din Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin sakataren jam’iyyar APC ta jihar Kano, Abdulsalami Ginsau ya rigamu gidan gaskiya a otal din Chida dake Utako, Abuja.

Rahoton yace Abdulsalami shine ke kula da masaukin baki na wakilan jam’iyyar APC daga jihar Kano a babban taron jam’iyyar da aka yi a Abuja.

Kuma ya je otal din inda kama duka dakunan otal din guda 150.

Saidai bayan da gari ya waye aka tafi wajan taron jam’iyyar APC din sai ba’a ganshi ba, anan aka fara bincike.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ya bayyana cewa, sun kai korafi ofishin ‘yansanda dake Utako, yace sai ‘yansandan suka ce an kawo musu rahoto daga Otal Chida, ko da suka je sai suka ga Abdulsalami ne.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: An ragewa wannan 'yarsandar Mukami saboda Bidiyon data watsa a kafafen sada zumunta

‘yansanda sun ce sun fara bincike kan lamarin.

Itama wata majiya daga otal din ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace An kama dakuna 150 na otal din amma wadanda suka je otal din sun kai mutane 1000.

Da suka yi korafi sai ake ce musu an kama otal din dukansa.

Majiyar ta kara da cewa da kanawan ke amfani da lifta sai ta lalace taki budewa amma suka yi amfani da karfi suka budeta.

Shine shi kuma Abdulsalami da ya shiga Liftar sai ta fada kasa dashi.

Majiyar tace har kowa ya tafi daga otal din ba’a lura da abinda ya faru dashi ba saida ya fara wari.

Karanta Wannan  Rahoto: Rashin aikin yi a tsakanin Matasan Qasar Amurka yayi Qamari, babu banbanci tsakanin masu Digiri da wadanda basu je makaranta ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *